A cewar kafar yada labarai ta Hauza, a ranar 27 Jumada Sani 1447 daidai da 17 Disamba 2025 Miladiyya, Jagora Imam Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) ya gana da daliban Hauza da ke karatu a Birnin Qum, tare da wasu daliban jami’a daga sauran garuruwa.
Wannan ganawar ta biyo bayan halartar wani babban taro ne na karrama ma’aikata da ke raya tunani da tafarkin Imam Khomeini (Qs) a fadin duniya.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Laraba 27 Jumada Sani 1447 (17/12/2025), shi ne irinsa na farko da aka shirya musamman don wannan manufa.
A yayin ganawar, Imam Zakzaky — kamar yadda aka saba — bayan ya gabatar da gajeren bayani kan dalilin zuwansa ƙasar Iran, ya yi wa daliban nasihohi masu cike da hikima kan yadda ya kamata su mayar da hankali wajen karatu da gudanar da aikace‑aikacen su duka bisa niyyar neman tagomashin Allah (SWT).
Sayyid Zakzaky (H) ya kammala jawabin nasa da yabawa yara, ’yan ayarin waka na “Abna’u Ruhullah”, waɗanda suka gabatar da wakar “Salam Farmande”, tare da yi musu fatan alheri.
A ƙarshe, Jagora ya rufe taron da addu’a, sannan ya sallami ’yan uwa cikin farin ciki da fatan alkhairi.
Daga Kafar Sadarwa ta Albasira, Qum — Iran.












Your Comment